Ajuji Ahmed ya sake dare kujerar shugabancin NNPP.
An sake zaɓen Ahmed ne a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar na ƙasa da ya gudana a Abuja, inda zai yi wa’adin shekaru huɗu karo na biyu.
Jam’iyyar ta kuma sake zaɓen sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kasa, ciki har da Abba Kawu, mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa; Onu Nwaze, mataimakin shugaban jam’iyyar na kudu; Dipo Olayokun, sakataren ƙasa; da Oladipo Johnson, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar.
Batola, mataimakin sakataren walwala na ƙasa; Bush Adomson, mataimakin mai binciken kuɗi na ƙasa; Saleh Bade, mataimakin sakataren kuɗi na ƙasa; da Chubisi Emmanuel, mataimakin ma’aji na ƙasa.
Shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar na ƙasa, Bala Mohammedo, ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa ƙa’ida da kuma dokoki da ƙa’idodin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta (INEC).
A nasa jawabin, Ahmed ya ce an “sake tsugunar da jam’iyyar, an sake tsarata kuma an ƙarfafa ta” a matsayin babbar mai ruwa da tsaki a tsarin dimokiraɗiyyar ƙasar nan.
Ya ce, “Idanun kowa na kan babbar jam’iyyarmu domin nuna hanyar da za a bi wajen samun dimokiraɗiyya mai ɗorewa da ci gaba a Najeriya.”
Shi ma da yake jawabi, Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP, ya yaba wa zaɓaɓɓun jami’an tare da yi musu kira da su kasance masu ladabi da biyayya ga jam’iyyar.


