NSC ta tabbatar da gidaje da ladan $100,000 ga Super Falcons da D’Tigress
Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC) ta tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen bayar da gidaje, lambar girmamawar ƙasa (national honours), da kuma kuɗaɗen lada da suka kai kimanin dala $100,000 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a bai wa Super Falcons da D’Tigress.


Shugaban NSC, Shehu Dikko, ya bayyana hakan ne a ƙasar Morocco, inda ya ce takardun gidaje da na lambar girmamawa sun riga sun kammala, yayin da ake kammala tsarin tura kuɗaɗen kai tsaye zuwa asusun bankin ’yan wasan.


An bayar da waɗannan lada ne domin girmama bajintar Super Falcons wajen lashe kofin WAFCON karo na 10, da kuma nasarar D’Tigress ta lashe kofin AfroBasket karo na biyar a jere.
Wannan mataki na nuna yadda gwamnatin tarayya ke ƙarfafa gwiwa da tallafa wa wasannin mata a Najeriya tare da karrama ƙwazon ’yan wasan da suka ɗaukaka tutar ƙasa a matakin nahiyar Afirka.