A zaman kotun na wannan rana, kotun ta mallakawa Iyalan Marigayi Alh Baballe Ila Garejin da ake ta faman takaddama a kansa, Wanda Marigayi Alh Baballe Ila ya rasu ya bari kuma Iyalan sa suka je kotu domin a raba musu Gado. Kwatsam sai wani Mai Suna Alh Yusuf Garba Ali ya bijiro yace, wannan Garejin Mallakin sa ne, inda yace Nasiru Baballe Ila ne ya sayar masa. Wane tudu wane Gangare akayi ta shiga kotu har kotuna 3 Ciki harda Babbar Kotun Daukaka kara dake Nan Kano Karkashin jagorancin Alkalin alkalai na kotunan shari’ar Addinin Musulunci. Karshe dai Babbar kotun Daukaka kara dake zaman ta a kano tayi hukunci ta Allon Gani – Ga ka inda ta tabbatar da hukuncin Babbar kotun Daukaka kara ta Addinin Musulunci, inda tace tun Asalin karar da akayi a Kotun Shari’ar Musulunci dake zaman ta a Gwagwarwa ba’a shigar da ita a dedai ba, Iyalan Marigayi Alh Baballe Ila sun Nemi a raba musu Gado sai kuma a hannu guda ake Gudanar da Chinikin Garejin tsakanin Nasiru Baballe Ila da Alh Yusuf Garba Ali. Inda a karshe ma, daga Cikin Magadan ba’a saka mace 1 a Cikin Neman rabon Gadon ba hasalima Babu inda magada suka sanya hannu akan anyi musu rabon Gadon, hakan ne tasa kotun ta Dogara da wadannan hujjoji ta yanke hukunci kan Magadan su koma kotun kasa ta raba musu Gado. A karshe dai munyi kokarin ji daga bangaren lauyoyin dake kare kowanne bangare da suka hadar da Barr Ibrahim Abdullahi Chedi dake tsayawa Nasiru Baballe Ila, sai Kuma Barr Hashim Ma’aruf dake tsayawa Alh Yusuf Garba Ali bamu samu ji daga garesu ba, Saidai Barr Abbas Sulaiman Magashi dake tsayawa Iyalan Marigayi Alh Baballe Ila ya tabbatar da hukuncin.


