Sanatan ya ce an mika cak ɗin ne a daren jiya a ofishinsa da ke Majalisar Tarayya a Abuja, a gaban wasu masu ruwa da tsaki daga jihar Kano. Ya bayyana cewa an hana Fa’izu Alfindiki haƙƙinsa ne saboda tsayuwarsa kan gaskiya, kare muradin talakawa da kuma biyayyarsa ga jam’iyyar APC.Sanata Barau ya bayyana lamarin a matsayin zalunci da tauye ’yancin dan kasa, yana mai cewa hakan barazana ce ga ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin shiga jam’iyyar siyasa. Ya jaddada cewa mutane irin su Fa’izu Alfindiki su ne ginshiƙan dimokuraɗiyya, kuma wajibi ne a rika kare su da ƙarfafa su a kowane lokaci.Da yake jawabi bayan karɓar cak ɗin, Hon. Fa’izu Alfindiki ya miƙa godiya ga Sanata Barau I. Jibril, yana mai cewa wannan mataki ya ƙara masa tabbaci cewa jam’iyyar APC jam’iyya ce da ke tsayawa tare da ’ya’yanta. Ya ce goyon bayan da aka nuna masa ya ƙarfafa masa gwiwa tare da tabbatar da cewa bai yi kuskuren tsayawa kan gaskiya ba.MairahotoUmar Abdullahi