Kungiyar lauyoyi ta NBA da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun bayyana damuwa kan zargin sauya dokokin haraji bayan amincewar majalisa Rahotanni sun nuna cewa sun ce akwai barazana ga sahihanci da gaskiyar aikin majalisa, tare da kiran a dakatar da aiwatar da dokokin nan take Majalisar tarayya ta kafa kwamitin mutum bakwai domin binciken zargin, yayin da ake kara rade-radin matsin lamba kan bangaren zartarwa karkashin Bola Tinubu.

A sakon da ya wallafa a X, Atiku Abubakar ya bayyana zargin sauye-sauyen a matsayin hari ga ikon majalisa, yana mai cewa hakan na nuna rashin mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya. Karafin NBA kan dokar harajin Tinubu A wata sanarwa da shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya fitar, kungiyar ta ce dole ne a gudanar da bincike a bayyane kuma ba tare da boye-boye ba, domin fayyace yadda aka amince da dokokin harajin. Shugaban NBA ya ce ya zama dole a dakatar da duk wani shiri na aiwatar da dokokin har sai an bincika kuma an warware dukkan wadannan zarge-zarge.

NBA ta kuma bayyana cewa rikicin da ke tasowa daga wannan ce-ce-ku-cen na iya girgiza yanayin kasuwanci, ya rage kwarin gwiwar masu zuba jari, tare da jefa ‘yan kasa da kamfanoni cikin rashin tabbas. Atiku ya fadi hadarin sauya dokar haraji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zargin shigar da wasu ka’idoji ba tare da amincewar majalisa ba na nuni da akwai babbar matsala.

Ya ce ana zargin bangaren zartarwa da kara tilastawa jama’a da kakabawa ‘yan kasa nauyi mai tsanani tare da cire hanyoyin sa ido kan jami’an haraji.

A halin yanzu dai majalisar wakilai ta kafa kwamiti bincike da zai tattara bayanai game da zargin da aka yi kan dokar harajin Tinubu.