Gwamnatin Tarayya ta ayyana . 25 da 26 ga Disamba da kuma 1 ga Janairu 2026, a matsayin ranakun hutu na ƙasa.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan inda ya ce an ba da hutu a waɗannan ranaku ne domin murnar Kirsimeti da rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti wato Boxing day da kuma sabuwar shekara.
Ministan ya yi kira ga ‘yan Najeriya “Da su yi tunani kan darajoji na soyayya da zaman lafiya da kuma sadaukarwa da murnar haihuwar Yesu Almasihu.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan ƙasa, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba, da su yi amfani da lokacin bukukuwa wajen addu’a don zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasa.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da “‘Su ci gaba da kiyaye doka da lura da tsaro a lokacin bukukuwan, yayin da ya yi masu fatan Kirsimeti mai albarka da sabuwar shekara mai albarka.”


