Har yanzu ana ci gaba da tafka muhawara kan yadda shugabannin hukumomin harkokin da suka shafi sarrafawa da tacewa da jigilar man fetur da gas na Najeriya suka ajiye aiki taƙaddama da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote.

A ranar 17 ga watan Disamba ne shugaban NMDPRA, Ahmed Farouk ya ajiye aikinsa a wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, inda ta ce tuni shugaba Tinubu ya aike da sunan mutumin da zai maye gurbinsa.

Sanarwar ta ce shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisar dattawa da ta amince da naɗin Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban hukumar ta NMDPRA.

Shi ma shugaban hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe ya sauka daga muƙaminsa, inda shi ma fadar shugaban ƙasar ta aike da sunan mutumin da zai gaje shi.

Murabun ɗinsu ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Aliko Dangote ya yi zargin cewa Farouk Ahmed na biya wa ƴaƴansa guda huɗu kuɗin makaranta a Switzerland da suka kai dala miliya biyar, har ma hukumar ICPC ta ce za ta ƙaddamar da bincike.