Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo,mai shekara 20, yana ganin ba shi da makoma a Manchester United karkashin jagorancin Ruben Amorim kuma zai yi tunanin barin kungiyarsa ta kuruciya a watan Janairu.(Mail – subscription required), external
Manchester United da Manchester City da Liverpool da kuma Tottenham sun fara tattaunawa da dan wasan Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25 game da barinsa Bournemouth a kan fam miliyan 65 ko dayake sai ya cimma ma matsaya da Bournemouth din a watan Janairu domin su iya siyansa. (The i – subscription required), external
Manchester United ta yi ammanar cewa Semenyo zai iya karfafa bangaren hagu na kungiyar yayin da Amorim ke nuna shakku kan dan wasan Denmark Patrick Dorgu, mai shekara 21, wanda aka sayo kan fan miliyan 25 a watan Fabarairu daga Leece.(Sun), external
Bournemouth na Kallon dan wasan Tottenham da yankin Wales Brennan Johnson,mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Semenyo. (Teamtalk), external
Sai dai watakila, Cherries su fuskanci goggaya daga Crystal Palace, wadanda sun nuna sha’awar daukar Johnson daga Spurs. (Guardian), external


