Dakarun sojin Najeriya na rundunar ‘Operation Hadin Kai’ sun samu nasarar cafke wasu motoci biyu kirar ‘pickup’ makare da kayayyakin masarufi da dabaru, wadanda ake kokarin kai wa mayakan kungiyar ta’adda ta ISWAP a jihar Borno.
Fitacciya Ta rawaito cewa, sojojin sun yi kicibis da motocin ne yayin da suke gudanar da sintirin yaki na musamman, inda suka tarar da motocin suna jigilar kayayyakin zuwa maboyar ‘yan ta’addan.
Rahotanni daga jaridar Punch sun bayyana cewa, ganin karfin wutar sojojin ya sa masu safarar kayan sun tsere zuwa cikin daji suka bar motocin da kayayyakin. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa motocin na dauke da abinci, man fetur, da sauran kayan bukata masu muhimmanci ga ‘yan ta’addan.
Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin ta kara kaimi wajen datse hanyoyin samar da kayayyaki ga ‘yan ta’addan, da nufin karya lagon su da kuma hana su samun damar ci gaba da kai hare-hare.


