Burkina Faso ta Saki Jirgin Sojin Sama na Najeriya da Mutum 11 da ta kama
Wata tawaga daga Najeriya ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ta gudanar da tattaunawar diflomasiyya da shugaban mulkin sojan Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, dangane da wani jirgin Sojin Sama na Najeriya kirar C-130 da ke ɗauke da mutane 11 wanda aka tsare a ƙasar.
Tattaunawar ta haifar da sakin mutanen 11 da kuma jirgin nan take.
Bayan haka, Minista Tuggar ya gana da Sojin Saman da aka sako domin tabbatar da lafiyarsu.
A halin yanzu, tawagar da sojojin suna kan hanyarsu ta komawa kasarnan
Najeriya ta jaddada bin ƙa’idojin sufurin jiragen sama na ƙasa da ƙasa, tare da nuna girmamawa ga ikon ƙasar Burkina Faso, sannan ta nisanta kanta daga duk wasu zarge-zargen cin zarafi da ba su da hujja.
Bangarorin biyu sun kuma jaddada kalubalen tsaro da suke fuskanta tare, da kuma muhimmancin kyakkyawar alaƙar a tsakaninsu.
Wannan warware aatsalar, ya nuna nasarar diflomasiyya wajen rage yuwuwar rikicin yankin.
Jirgin sojan ya yi saukar gaggawa a birnin Bobo-Dioulasso na Burkina Faso a ranar 8 ga Disamba, 2025, sakamakon matsalar fasaha.
Hukumomin Burkina Faso sun tsare mutanen tare da kwace jirgin, suna zargin cewa jirgin ya shiga sararin samaniyarsu ba tare da izini ba.


