Dimbin Masoya Fitaccen Shirin nan me dogon Zango Watau (Labarina) Wanda Fitaccen Darakta Mal. Aminu Saira Yake gabatarwa Sunyi Allah Wadai tare da takaicin ganin Wata Sabuwar Jaruma Acikin Shirin.
Mutane da dama ne Suka Nuna damuwarsu tare da Korafe korafe tun bayan ganin Fuskar Sabuwar Jarumar Acikin Shirin, inda Suka bayyana cewar Sam bai dace Mal. Aminu Saira Ya Sakata Acikin Shirin ba Kasancewar tayi Kaurin Suna a Shafukan Sada Zumunta Wajen Yada Bidiyoyi na rashin da’a tare da Maganganun b*tsa.
A Yanzu Haka dai Masoya Shirin sun bayyana lallai Sai dai Mal. Aminu Saira Ya Maye gurbinta da wata ko Kuma Ya cireta gaba daya.
Meye ra’ayinku akan Wannan?


