Shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da BBC ƙara a kotu inda yake neman a biya shi diyyar kuɗi dala biliyan biyar, wato kwatankwacin naira tiriliyan 7,265,798,622,555, kan wani rahoto na musamman da kafar ta yaɗa game da jawabinsa na ranar 6 ga watan Janairun 2021.
Trump na zargin BBC ne kan ɓata suna da karya ƙa’idar aiki, kamar yadda bayanan ƙarar daya shigar a jihar Florida suka nuna
BBC ta nemi afuwar Trump a watan da ta gabata, sai dai ta yi watsi da batun biyan diyya da kuma zargin cewa rahoton “ya ɓata sunan” shugaban ƙasar.
Lauyoyin Trump na zargin BBC da ɓata masa suna ta hanyar “yanke bayanin da yayi da mummunar manufa”.
Har yanzu BBC ba ta mayar da martani kan ƙarar ba.


