Jihar Adamawa Za Ta Kafa Sabbin Sarakunan Gargajiya Uku
Majalisar dokokin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta amince da wani kuduri na kafa sabbin masarautu guda uku a jihar. Wannan shawarar ta zo ne kwanaki kadan bayan Gwamna Ahmadu Fintiri ya rattaba hannu kan dokar kafa sabbin unguwanni 84 a ranar 4 ga watan Disamba.
A cikin wata wasika da gwamnan ya aikewa majalisar, ya bukaci amincewarsu da kudurin da ya shafi nada sarakuna da sauke su, wanda zai ba shi damar kirkiro sabbin masarautu da nada ko tsige sarakuna kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Kudurin ya yi karatu na daya da na biyu a zauren majalisar a ranar Litinin din da ta gabata, daga bisani kuma aka amince da shi a ranar Talata, inda a yanzu ake jiran sa hannun gwamnan ya zama doka.
Bugu da kari, wannan sabuwar doka ta tsige Lamidon Adamawa Mustapha Barkindo a matsayin shugaban majalisar sarakunan Adamawa na din-din-din, wanda hakan ke nufin yanzu zai rika karba-karba a tsakanin masu rike da sarautun gargajiya na jihar.
A dokar farko da gwamnan ya sanya wa hannu, an rage yawan kananan hukumomin da ke karkashin Lamidon Adamawa daga takwas zuwa uku. A baya dai kananan hukumomin Hong, Song, Gombi, Fufore, Girei, Yola North, Yola South, da Mayo-Belwa sun fada karkashin masarautar Adamawa, amma yanzu Girei, Jimeta, da Yola ne kawai suka rage a karkashin wannan ikon.