Obasanjo, Atiku, da sauransu sun halarci daurin auren diyar Kwankwaso a Kano
Manyan mutane da suka hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar Asabar din da ta gabata sun halarci daurin auren diyar tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a siyasar Kwankwasiyya Sanata Rabiu Kwankwaso.
Kwankwaso ya aurar da diyarsa, Dr Aishatu Kwankwaso da Fahad, dan hamshakin dan kasuwan nan mazaunin Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.
Sauran wadanda suka halarci daurin auren akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Daurin auren wanda ya gudana a fadar mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, babban limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen ne ya yi.
Sauran mutanen da suka halarci daurin auren sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul Ningi da Sanata Adamu Aliero wanda kuma tsohon gwamnan jihar Kebbi ne.
Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Edo Lucky Igbinedion, Mahamud Shinkafi, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Isah Yuguda, tsohon gwamnan jihar Bauchi, Victor Attah, tsohon gwamnan Akwa Ibom, da Cif Achike Udenwa, tsohon gwamnan jihar Imo.