Jami’an mu, tare da ma’aikata daga sauran hukumomin ‘yan uwa, suna aiki ba dare ba rana don samar da tsaro da walwala ga duk wanda abin ya shafa. Hakazalika muna yaba wa mutanen jihar nagari wadanda suke aiki da radin kansu wajen bayar da agajin jin kai.