A wani sabon rikici tsakanin Elon Musk, mamallakin kamfanin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) da wani alkali a Brazil, gwamnatin kasar ta fara toshe shafin X daga aiki.
Wannan matakin ya biyo bayan umarnin da wani alkali na Kotun Koli ta Brazil, Alexandre de Moraes, ya bayar na dakatar da X saboda kin bin umarnin da aka bayar kan batun yada labaran karya da kuma rashin nada wakili a kasar.
Wannan rikici ya kara dagula alakar da ke tsakanin Musk da alkalin, wanda a baya ya soki Musk kan kin goge wasu sakonni da ake ganin suna yada labaran karya da kuma tunzura jama’a.
A halin yanzu dai, ‘yan kasar Brazil da dama sun wayi gari ba tare da samun damar shiga shafin X ba, lamarin da ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta daban-daban. Musk ya bayyana cewa wannan matakin “abin takaici ne” kuma “ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki.”
Muna ci gaba da bibiyar lamarin domin kawo muku cikakken rahoto.